Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 10:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

2. To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya,

3. da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza,

4. da Saminu Bakan'ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.

5. Su sha biyun nan ne Yesu ya aika, ya yi musu umarni, ya ce, “Kada ku shiga ƙasar al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa.

6. Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama'ar Isra'ila,Irm

7. kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’

8. Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta.

9. Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku,

10. kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci hakkinsa.

11. Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi.

12. In za ku shiga gidan ku ce, ‘Salama alaiku.’

13. In gidan na kirki ne, salamarku tă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tă komo muku.

14. Kowa kuma ya ƙi yin na'am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku.

Karanta cikakken babi Mat 10