Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 1:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya,

10. Hezekiya ya haifi Manassa, Manassa ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya.

11. Yosiya ya haifi Yekoniya da 'yan'uwansa, wato, a lokacin da aka ɗebe su zuwa Babila.

12. Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Shayeltiyel ya haifi Zarubabel,

13. Zarubabel ya haifi Abihudu, Abihudu ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azuro,

14. Azuro ya haifi Saduƙu, Saduƙu ya haifi Akimu, Akimu ya haifi Aliyudu,

15. Aliyudu ya haifi Ele'azara, Ele'azara ya haifi Matana, Matana ya haifi Yakubu,

16. Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Almasihu.

17. Wato, dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Daga ɗebe su zuwa Babila zuwa kan Almasihu, zuriya goma sha huɗu.

18. Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa'ad da Yusufu yake tashin Maryamu mahaifiyar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki.

Karanta cikakken babi Mat 1