Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 1:17-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Wato, dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Daga ɗebe su zuwa Babila zuwa kan Almasihu, zuriya goma sha huɗu.

18. Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa'ad da Yusufu yake tashin Maryamu mahaifiyar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki.

19. Yusufu mijinta kuwa da yake shi mutumin kirki ne, ba ya kuma so ya ba ta kunya a gaban jama'a, sai ya yi niyyar rabuwa da ita a asirce.

20. Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.

21. Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”

22. An yi wannan ne duk, don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa,

23. “Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa,Za a kuma sa masa suna Immanuwel.”(Ma'anar Immanuwel kuwa itace Allah na tare da mu.)

24. Da Yusufu ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala'ikan Ubangiji, ya ɗauki matarsa,

25. amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.

Karanta cikakken babi Mat 1