Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 9:3-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. tufafinsa suka yi fari fat suna sheƙi, yadda ba mai wankin da zai iya yinsu haka a duniya.

4. Sai Iliya da Musa sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu.

5. Sai Bitrus ya sa baki, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin, mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.”

6. Ya rasa abin da zai faɗa ne, don sun tsorata da gaske.

7. Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena. Ku saurare shi.”

8. Farat haka da suka dudduba, ba su ƙara ganin kowa ba, sai Yesu kaɗai tare da su.

9. Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.

10. Sai suka bar maganar yasu-yasu, suna tambayar juna komece ce ma'anar tashi daga matattu.

11. Suka tambaye shi suka ce, “To, yaya kuwa malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya yă fara zuwa?”

12. Sai ya ce musu, “Lalle ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwa. Yaya kuwa yake a rubuce a kan Ɗan Mutum, cewa zai sha wuya iri iri, a kuma wulaƙanta shi?

13. Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, sun kuma yi masa abin da suka ga dama, yadda labarinsa yake a rubuce.”

14. To, da suka komo wurin almajiran, sai suka ga babban taro ya kewaye su, malaman Attaura kuma na muhawara da su.

15. Da ganin Yesu sai duk taron suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ɗungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi.

16. Ya tambaye su, “Muhawarar me kuke yi da su?”

17. Sai ɗaya daga cikin taron ya amsa masa ya ce, “Malam, ga shi, na kawo maka ɗana, don yana da beben aljan.

Karanta cikakken babi Mar 9