Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 7:8-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Kuna yar da umarnin Allah, kuna riƙe da al'adun mutane.”

9. Sai ya ce musu, “Lalle kun iya yar da umarnin Allah don ku bi al'adunku!

10. Domin Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ da kuma, ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa, sai lalle a kashe shi.’

11. Amma ku kukan ce, ‘In mutum ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni ya zama Korban,” ’ (wato an sadaukar),

12. shi ke nan fa, ba saura ku bar shi ya yi wa ubansa ko uwa tasa aikin kome.

13. Ta haka kuke banzanta Maganar Allah ta wajen al'adunku na gargajiya. Kun kuwa cika yin irin waɗannan abubuwa.”

14. Sai ya sāke kiran jama'a, yă ce musu, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimta.

15. Ba abin da yake shiga mutum daga waje yă ƙazanta shi, sai abin da yake fita, yake ƙazanta shi. [

16. Duk mai kunnen ji, yă ji.]”

17. Bayan rabuwarsa da taron, da ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi ma'anar misalin.

18. Ya ce musu, “Ashe, ku ma ba ku da fahimta ne? Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum daga waje, ba yadda zai ƙazanta shi,

19. tun da yake ba zuciya tasa ya shiga ba, cikinsa ne, ta haka kuma zai fita?” Ta haka Yesu ya halatta kowane irin abinci.

20. Ya kuma ce, “Abin da yake fita daga cikin mutum yake ƙazanta shi.

21. Don daga ciki ne, wato daga zuciyar mutum, mugayen tunani yake fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina,

22. da kwaɗayi, da mugunta, da ha'inci, da fajirci, da kishi, da yanke, da girmankai, da kuma wauta.

Karanta cikakken babi Mar 7