Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 7:21-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Don daga ciki ne, wato daga zuciyar mutum, mugayen tunani yake fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina,

22. da kwaɗayi, da mugunta, da ha'inci, da fajirci, da kishi, da yanke, da girmankai, da kuma wauta.

23. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga ciki suke fitowa, suna kuwa ƙazanta mutum.”

24. Daga nan kuma ya tashi ya tafi wajajen Taya da Sidon. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa ya sani ba, amma ba ya ɓoyuwa.

25. Nan da nan sai wata mace, wadda 'ya tata ƙarama take da baƙin aljan ta ji labarinsa, ta zo ta fāɗi a gabansa.

26. Matar kuwa Baheleniya ce, asalinta kuma Basurofinikiya ce. Sai ta roƙe shi ya fitar wa 'ya tata da aljanin.

27. Yesu ya ce mata, “Bari 'ya'ya su ƙoshi tukuna, domin bai kyautu a bai wa karnuka abincinsu ba.”

28. Amma ta amsa masa ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”

29. Sai ya ce mata, “Saboda wannan magana taki, koma gida, aljanin, ai, ya rabu da 'yarki.”

30. Sai ta koma gida ta iske yarinyar a kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.

31. Sai ya komo daga wajen Taya, ya bi ta Sidon ya je Tekun Galili ta Dikafolis.

32. Suka kawo masa wani kurma mai i'ina, suka roƙe shi ya ɗora masa hannu.

33. Yesu ya ɗauke shi suka koma waje ɗaya, rabe da taron, ya sa yatsotsinsa a kunnuwansa, ya tofar da yau, ya kuma taɓa harshensa.

34. Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuciya, sai ya ce masa, “Iffata!” wato “Buɗu!”

Karanta cikakken babi Mar 7