Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 6:6-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu.Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.

7. Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu.

8. Ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko gurasa, ko burgami, ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai,

9. amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu.

10. Ya ce musu, “Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.

11. Duk inda aka ƙi yin na'am da ku, aka kuma ƙi sauraronku, in za ku tashi, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunka don shaida a kansu.”

12. Haka fa, suka fita, suna wa'azi mutane su tuba.

13. Suka fitar da aljannu da yawa, suka kuma shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka warkar da su.

14. Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”

15. Amma waɗansu kuwa suka ce, “Iliya ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawa.”

16. Amma da Hirudus ya ji haka, sai ya ce, “Yahaya, wanda na fille wa kai, shi ne aka tasa.”

17. Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yahaya, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan'uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura.

18. Don dā Yahaya ya ce wa Hirudus, “Bai halatta ka zauna da matar ɗan'uwanka ba.”

19. Hirudiya kuwa na riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba,

20. don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa'ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake na murna da jinsa.

21. Amma wani sanadi ya zo, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, ya yi wa hakimansa, da sarakunan yaƙinsa, da kuma manyan ƙasar Galili biki.

Karanta cikakken babi Mar 6