Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 6:30-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Manzannin suka komo wurin Yesu, suka faɗa masa duk iyakar abin da suka yi, da abin da suka koyar.

31. Ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita a wurin da ba kowa, ku ɗan huta.” Domin mutane da yawa suna kaiwa suna kawowa, ko damar cin abinci ma, manzannin ba su samu ba.

32. Sai suka tafi cikin jirgi wurin da ba kowa, su kaɗai.

33. Ashe, mutane da yawa sun ga tafiyarsu, sun kuwa shaida su, suka fa dunguma ta tudu daga garuruwa duka, suka riga su zuwa.

34. Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke ba makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa.

35. Kusan faɗuwar rana sai almajiransa suka zo gare shi, suka ce masa, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta kusa fāɗuwa.

36. Sai ka sallame su, su shiga karkara da ƙauyuka na kurkusa, su saya wa kansu abinci.”

37. Amma ya amsa musu ya ce, “Ku ku ba su abinci mana.” Sai suka ce masa, “Wato mu je mu sayo gurasa ta dinari metan, mu ba su su ci?”

38. Ya ce musu, “Gurasa nawa gare ku? Ku je ku dubo.” Da suka binciko suka ce, “Ai, biyar ne, da kifi biyu.”

39. Sa'an nan ya yi umarni dukkansu su zazzauna ƙungiya ƙungiya a ɗanyar ciyawa.

40. Haka suka zauna jeri jeri, waɗansu ɗari ɗari, waɗansu hamsin hamsin.

41. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu.

Karanta cikakken babi Mar 6