Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 5:34-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, ki warke daga cutarki.”

35. Yana cikin magana, sai ga waɗansu daga gidan shugaban majami'a suka ce, “Ai, 'yarka ta rasu, me kuma za ka wahalar da Malamin?”

36. Amma Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, ya ce wa shugaban majami'a, “kada ka ji tsoro, ka ba da gaskiya kawai.”

37. Bai bar kowa ya bi shi ba sai Bitrus, da Yakubu, da kuma Yahaya ɗan'uwan Yakubu.

38. Da suka isa gidan shugaban majami'a, ya ji ana hayaniya, ana kuka, ana kururuwa ba ji ba gani.

39. Da kuma ya shiga, ya ce musu, “Don me kuke hayaniya kuna kuka haka? Ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.”

40. Sai suka yi masa dariyar raini. Shi kuma bayan ya fitar da su duka waje, sai ya ɗauki uban yarinyar, da uwa tata, da kuma waɗanda suke tare da shi, ya shiga inda yarinyar take.

41. Ya kama hannunta, ya ce mata, “Talita ƙumi”, wato, “Ke yarinya, ina ce miki, tashi.”

42. Nan take yarinyar ta tashi ta yi tafiya, domin 'yar shekara goma sha biyu ce. Nan da nan kuwa mamaki ya kama su.

43. Sai ya kwaɓe su matuƙa kada kowa ya ji wannan labari. Ya kuma yi umarni a ba ta abinci.

Karanta cikakken babi Mar 5