Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 5:25-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini,

26. ta kuma sha wahala da gaske a hannun masu magani da yawa, har ta ɓad da duk abin da take da shi, amma duk a banza, sai ma gaba-gaba cutar take yi.

27. Da ta ji labarin Yesu, ta raɓo ta bayansa cikin taron, ta taɓa mayafinsa.

28. Don tā ce a ranta, “Ko da tufarsa ma na taɓa, sai in warke.”

29. Nan take zubar jininta ta tsaya, ta kuma ji a jikinta an warkar da cutarta.

30. Nan da nan kuwa da Yesu ya ji wani iko ya fita daga gare shi, sai ya waiwaya a cikin taron, ya ce, “Wa ya taɓa tufata?”

31. Sai almajiransa suka ce masa, “Kana ganin taro na matsarka, ka ce, wa ya taɓa ka?”

32. Sai Yesu ya juya domin ya ga wadda ta yi haka.

33. Matar kuwa da ta san abin da aka yi mata, sai ta zo a tsorace, tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta faɗa masa ƙashin gaskiya.

34. Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, ki warke daga cutarki.”

Karanta cikakken babi Mar 5