Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 5:16-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Waɗanda aka yi abin a kan idonsu kuwa, suka farfaɗi abin da ya gudana ga mai aljannun da kuma aladen.

17. Sai suka fara roƙon Yesu ya bar musu ƙasarsu.

18. Yana shiga jirgi ke nan, sai mai aljannun nan a dā ya roƙe shi izinin zama a gunsa.

19. Amma Yesu bai yardar masa ba, ya ce masa, “Tafi gida wurin 'yan'uwanka, ka faɗa musu irin manyan abubuwan da Ubangiji ya yi maka, da kuma yadda ya ji tausayinka.”

20. Sai ya tafi, ya shiga baza labari a Dikafolis na irin manyan abubuwan da Yesu ya yi masa. Duk mutane kuwa suka yi al'ajabi.

21. Da Yesu ya sāke haye ƙetare cikin jirgi, sai babban taro ya kewaye shi. Shi kuwa yana bakin tekun.

22. Sai ga wani daga cikin shugabannin majami'a, mai suna Yayirus. Da ganin Yesu kuwa ya fāɗi a gabansa,

23. ya roƙe shi da gaske, yana cewa, “'Yata ƙaramar tana bakin mutuwa. Idan dai a ce ka zo ka ɗora mata hannu, sai ta warke ta rayu.”

24. Sai suka tafi tare. Babban taro kuwa na biye da shi, suna matsa tasa.

25. Sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini,

26. ta kuma sha wahala da gaske a hannun masu magani da yawa, har ta ɓad da duk abin da take da shi, amma duk a banza, sai ma gaba-gaba cutar take yi.

27. Da ta ji labarin Yesu, ta raɓo ta bayansa cikin taron, ta taɓa mayafinsa.

28. Don tā ce a ranta, “Ko da tufarsa ma na taɓa, sai in warke.”

29. Nan take zubar jininta ta tsaya, ta kuma ji a jikinta an warkar da cutarta.

30. Nan da nan kuwa da Yesu ya ji wani iko ya fita daga gare shi, sai ya waiwaya a cikin taron, ya ce, “Wa ya taɓa tufata?”

31. Sai almajiransa suka ce masa, “Kana ganin taro na matsarka, ka ce, wa ya taɓa ka?”

32. Sai Yesu ya juya domin ya ga wadda ta yi haka.

33. Matar kuwa da ta san abin da aka yi mata, sai ta zo a tsorace, tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta faɗa masa ƙashin gaskiya.

34. Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, ki warke daga cutarki.”

Karanta cikakken babi Mar 5