Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 5:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Suka iso hayin teku a ƙasar Garasinawa.

2. Da saukarsa daga jirgin, sai ga wani mai baƙin aljan daga makabarta ya tarye shi.

3. Shi kuwa makabarta ce mazauninsa. Ba mai iya ɗaure shi kuma, ko da sarƙa ma.

4. Don dā an sha ɗaure shi da mari da sarƙa, amma ya tsintsinka sarƙar, ya gutsuntsuna marin, har ma ba mai iya bi da shi.

5. Kullum kuwa dare da rana yana cikin makabarta, da kan duwatsu, yana ta ihu, yana kukkuje jikinsa da duwatsu.

6. Da dai ya hango Yesu, sai ya sheƙo a guje ya fāɗi a gabansa,

7. ya ƙwala ihu ya ce, “Ina ruwanka da ni, Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Na gama ka da Allah, kada ka yi mini azaba.”

8. Ya faɗi haka ne domin Yesu ya ce masa, “Rabu da mutumin nan, kai wannan baƙin aljan!”

9. Yesu ya tambaye shi, “Me sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Tuli, don muna da yawa.”

10. Sai ya roƙi Yesu da gaske kada ya kore su daga ƙasar.

11. To, wurin nan kuwa da wani babban garken alade na kiwo a gangaren dutsen.

12. Aljannun nan suka roƙe shi suke ce, “Tura mu wajen aladun nan, mu shiga su.”

13. Ya kuwa yardar musu. Sai baƙaƙen aljannun suka fita, suka shiga aladun. Garken kuwa wajen alade dubu biyu, suka rugungunto ta gangaren, suka fāɗa tekun, suka halaka a ruwa.

14. Daga nan sai 'yan kiwon aladen suka gudu, suka ba da labari birni da ƙauye. Jama'a suka zo su ga abin da ya auku.

15. Da suka zo wurin Yesu suka ga mai aljannun nan a zaune, saye da tufa, cikin hankalinsa kuma, wato mai aljannun nan masu yawa a dā, sai suka tsorata.

16. Waɗanda aka yi abin a kan idonsu kuwa, suka farfaɗi abin da ya gudana ga mai aljannun da kuma aladen.

Karanta cikakken babi Mar 5