Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 4:19-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. amma taraddadin duniya, da jarabar dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga su sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.

20. Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, su ne kwatancin waɗanda suke jin Maganar, su karɓa, su kuma amfana, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”

21. Sai ya ce musu, “Shin, ana kawo fitila don a rufe ta da masaki, ko a ajiye ta a ƙarƙashin gado ne, ba don a ɗora ta a kan maɗorinta ba?

22. Ba abin da yake ɓoye, sai domin a bayyana shi a gaba. Ba kuma wani abin da yake asiri, sai domin a bayyana shi a gaba.

23. In da mai kunnen ji, yă ji.”

24. Sai ya ce musu, “Ku ji. Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.

25. Domin mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.”

26. Ya ce kuma, “Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a ƙasa.

27. A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma, bai kuwa san ta yadda aka yi ba.

28. Ƙasa da kanta takan ba da amfani, tsiro shi ne na farko, sa'an nan kai, sai kuma ƙwaƙƙwarar ƙwaya a kan.

29. Sa'ad da amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi ke nan.”

30. Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulkin Allah? Ko kuwa da wane misali za mu misalta shi?

31. Kamar ƙwayar mastad da yake, wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi ƙanƙantar ƙwayoyi a duniya,

32. duk da haka in an shuka ta, sai ta girma ta fi duk sauran ganye, ta yi manyan rassa, har tsuntsaye su iya sauka a inuwarta.”

33. Da misalai da yawa irin waɗannan Yesu ya yi musu Maganar Allah, daidai gwargwadon ganewa tasu.

34. Ba ya faɗa musu kome sai da misali, amma a keɓe yakan bayyana wa almajiransa kome.

Karanta cikakken babi Mar 4