Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Misali da Mai Shuka

1. Ya kuma fara koyarwa a bakin teku ke nan, sai babban taro ya haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi a tekun, ya kuwa zauna a ciki. Duk taron kuwa na kan tudu a bakin tekun.

2. Sai ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A cikin koyarwa tasa har ya ce musu,

3. “Ku saurara! Wani mai shuka ya tafi shuka.

4. Yana cikin yafa iri, sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su.

5. Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa.

6. Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe.

7. Waɗansu kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙayar ta tashi ta sarƙe su, ba su yi tsaba ba.

8. Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi yabanya, suka girma, suka yi tsaba, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”

9. Sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Manufar Misalan

10. Da suka kaɗaita, masu binsa da su sha biyun nan suka tambaye shi ma'anar misalan.

11. Sai ya ce musu, “Ku kam, an yardar muku ku san asirin Mulkin Allah, amma ga waɗanda ba sa cikinku, kome sai a cikin misali,

12. don gani da ido kam, su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba, wai don kada su juyo a yafe musu.”

Yesu Ya Ba da Bayanin Misalin Mai Shuka

13. Ya ce musu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misali ba? Ƙaƙa za ku fahimci sauran ke nan?

14. Mai shukan nan fa Maganar Allah yake shukawa.

15. Waɗanda suka fāda a hanya kuwa, su ne kwatancin waɗanda aka shuka Maganar a zuciya tasu. Da zarar sun ji, nan da nan sai Shaiɗan ya zo ya ɗauke Maganar da aka shuka a zuciya tasu.

16. Haka kuma waɗanda aka shuka a wuri mai duwatsu, su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar sai su karɓa da farin ciki.

17. Su kam, ba su da tushe, rashin ƙarƙo gare su, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru domin wannan Magana, nan da nan sai su yi tuntuɓe.

18. Waɗansu kuma su ne kwatancin waɗanda suka fāɗa cikin ƙaya, su ne waɗanda suke jin Maganar,

19. amma taraddadin duniya, da jarabar dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga su sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.

20. Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, su ne kwatancin waɗanda suke jin Maganar, su karɓa, su kuma amfana, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”

Fitila a Rufe da Masaki

21. Sai ya ce musu, “Shin, ana kawo fitila don a rufe ta da masaki, ko a ajiye ta a ƙarƙashin gado ne, ba don a ɗora ta a kan maɗorinta ba?

22. Ba abin da yake ɓoye, sai domin a bayyana shi a gaba. Ba kuma wani abin da yake asiri, sai domin a bayyana shi a gaba.

23. In da mai kunnen ji, yă ji.”

24. Sai ya ce musu, “Ku ji. Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.

25. Domin mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.”

Misali na Irin da ya Tsiro

26. Ya ce kuma, “Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a ƙasa.

27. A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma, bai kuwa san ta yadda aka yi ba.

28. Ƙasa da kanta takan ba da amfani, tsiro shi ne na farko, sa'an nan kai, sai kuma ƙwaƙƙwarar ƙwaya a kan.

29. Sa'ad da amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi ke nan.”

Misali na Ƙwayar Mastad

30. Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulkin Allah? Ko kuwa da wane misali za mu misalta shi?

31. Kamar ƙwayar mastad da yake, wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi ƙanƙantar ƙwayoyi a duniya,

32. duk da haka in an shuka ta, sai ta girma ta fi duk sauran ganye, ta yi manyan rassa, har tsuntsaye su iya sauka a inuwarta.”

Yesu Ya Yi Amfani da Misalai

33. Da misalai da yawa irin waɗannan Yesu ya yi musu Maganar Allah, daidai gwargwadon ganewa tasu.

34. Ba ya faɗa musu kome sai da misali, amma a keɓe yakan bayyana wa almajiransa kome.

Yesu Ya Tsawata wa Hadiri

35. A ran nan da maraice ya ce musu, “mu haye can ƙetare.”

36. Da suka bar taron, suka tafi da shi yadda yake a cikin jirgin, waɗansu jirage kuma na tare da shi.

37. Sai babban hadari mai iska ya taso, raƙuman ruwa kuma na ta fantsama cikin jirgin, har jirgin ya tasar wa cika da ruwa.

38. Yesu kuwa na daga ƙarshen baya na jirgin a kan matashi, yana barci. Sai suka tashe shi, suka ce masa, “Malam, za mu hallaka ba ka kula ba ko?”

39. Sai ya farka, ya tsawata wa iskar, ya kuma ce wa ruwan tekun, “Natsu! Ka yi shiru!” Sai iskar ta kwanta, wurin duk ya yi tsit.

40. Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”

41. Sai suka tsorata, matuƙar tsoro, suka ce wa juna, “Wa ke nan kuma, wanda har iska da ruwan teku ma suke yi masa biyayya?”