Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 4:11-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sai ya ce musu, “Ku kam, an yardar muku ku san asirin Mulkin Allah, amma ga waɗanda ba sa cikinku, kome sai a cikin misali,

12. don gani da ido kam, su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba, wai don kada su juyo a yafe musu.”

13. Ya ce musu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misali ba? Ƙaƙa za ku fahimci sauran ke nan?

14. Mai shukan nan fa Maganar Allah yake shukawa.

15. Waɗanda suka fāda a hanya kuwa, su ne kwatancin waɗanda aka shuka Maganar a zuciya tasu. Da zarar sun ji, nan da nan sai Shaiɗan ya zo ya ɗauke Maganar da aka shuka a zuciya tasu.

16. Haka kuma waɗanda aka shuka a wuri mai duwatsu, su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar sai su karɓa da farin ciki.

17. Su kam, ba su da tushe, rashin ƙarƙo gare su, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru domin wannan Magana, nan da nan sai su yi tuntuɓe.

18. Waɗansu kuma su ne kwatancin waɗanda suka fāɗa cikin ƙaya, su ne waɗanda suke jin Maganar,

19. amma taraddadin duniya, da jarabar dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga su sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.

20. Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, su ne kwatancin waɗanda suke jin Maganar, su karɓa, su kuma amfana, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”

21. Sai ya ce musu, “Shin, ana kawo fitila don a rufe ta da masaki, ko a ajiye ta a ƙarƙashin gado ne, ba don a ɗora ta a kan maɗorinta ba?

22. Ba abin da yake ɓoye, sai domin a bayyana shi a gaba. Ba kuma wani abin da yake asiri, sai domin a bayyana shi a gaba.

23. In da mai kunnen ji, yă ji.”

24. Sai ya ce musu, “Ku ji. Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.

25. Domin mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.”

Karanta cikakken babi Mar 4