Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 15:7-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Akwai wani wai shi Barabbas da yake ɗaure, tare da waɗansu 'yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin tawayen.

8. Jama'a fa suka matso, suka fara roƙon Bilatus ya yi musu abin da ya saba yi.

9. Sai ya amsa musu, ya ce, “Wato kuna so ne in sakar muku Sarkin Yahudawa?”

10. Don ya gane, saboda hassada ne manyan firistoci suka bashe shi.

11. Amma manyan firistocin suka zuga jama'a, gwamma ya sakar musu Barabbas.

12. Sai Bilatus ya sāke ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da wanda kuke kira Sarkin Yahudawa?”

13. Sai suka sāke yin ihu suka ce, “A gicciye shi!”

14. Bilatus ya ce musu, “Ta wane hali? Wane mugun abu ne ya yi?” Amma su, sai ƙara ɗaga murya suke yi, suna cewa, “A gicciye shi!”

15. Bilatus kuwa da yake yana son ƙayatar da jama'a, ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, ya ba da shi a gicciye shi.

16. Sai soja suka tafi da shi cikin fada, wato fadar mai mulkin, suka tara dukkan rundunar soja.

17. Suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura, suka kuma yi wani kambi na ƙaya, suka sa masa a kā.

18. Sai suka fara gaishe shi, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!”

19. Suka riƙa ƙwala masa sanda a ka, suna tattofa masa yau, sa'an nan suka durƙusa, wai suna masa ladabi.

20. Da suka gama yi masa ba'a haka, suka yaye masa alkyabba mai ruwan jar garura, suka sa masa nasa tufafi, suka kai shi waje don su gicciye shi.

21. Sai ga wani mai wucewa, wai shi Saminu Bakurane, uban Iskandari da Rufas, yana zuwa daga ƙauye. Suka fa tilasta masa ya ɗauki gicciyen Yesu.

22. Suka kai Yesu wani wuri wai shi Golgota, wato wurin ƙoƙon kai.

23. Suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, amma ya ƙi sha.

24. Sa'an nan suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu, suna kuri'a a kansu, su ga abin da kowa zai samu.

25. Da ƙarfe tara na safe suka gicciye shi.

26. Aka kuma rubuta sanarwar laifinsa sama da shi, wato “Sarkin Yahudawa.”

27. Suka kuma gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya dama da shi, ɗaya kuma a hagun. [

Karanta cikakken babi Mar 15