Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 14:4-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Waɗansu kuwa da suka ji haushi, suka ce wa juna, “Mene ne na ɓata mai haka?

5. Gama da ma an sayar da shi fiye da dinari ɗari uku, an ba gajiyayyu!” Sai suka hasala da ita, suna gunaguni.

6. Amma Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Don me kuke damunta? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.

7. Kullum kuna tare da gajiyayyu, ko yaushe kuma kuke so, kwa iya yi musu alheri, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.

8. Ta yi iyakacin ƙoƙarinta. Ta shafe jikina da mai gabannin jana'izata.

9. Hakika kuwa ina gaya muku, duk inda za a yi bishara a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa domin tunawa da ita.”

10. Sai Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin sha biyun nan, ya je wurin manyan firistoci don ya bashe shi a gare su.

11. Da suka ji haka suka yi murna, har suka yi alkawarin su ba shi kuɗi. Shi kuwa ya riƙa neman hanyar bashe shi.

12. A ranar farko ta idin abinci marar yisti, wato ran da aka saba yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa, sai almajiransa suka ce masa, “Ina kake so mu je mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?”

13. Sai ya aiki almajiransa biyu, ya ce musu, “Ku shiga gari, can za ku gamu da wani mutum ɗauke da tulun ruwa, ku bi shi.

14. Duk gidan da ya shiga, ku ce wa maigidan, ‘In ji Malam, ina masaukin da zai ci Idin Ƙetarewa da almajiransa?’

15. Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.”

16. Sai almajiran suka tashi, suka shiga gari, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Idin Ƙetarewa.

17. Da magariba ta yi, sai ya zo tare da sha biyun nan.

18. Suna cin abinci ke nan, sai Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni, wanda muke ci tare.”

Karanta cikakken babi Mar 14