Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 14:17-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Da magariba ta yi, sai ya zo tare da sha biyun nan.

18. Suna cin abinci ke nan, sai Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni, wanda muke ci tare.”

19. Suka fara baƙin ciki, suna ce masa da ɗaya ɗaya, “Ni ne?”

20. Sai ya ce musu, “Ɗaya daga cikin sha biyun nan ne dai, wanda muke ci ƙwarya ɗaya.

21. Ga shi, Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kuwa, kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”

22. Suna cikin cin abinci, sai ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Ungo, wannan jikina ne.”

23. Sai ya ɗauki ƙoƙo kuma, bayan ya yi godiya ga Allah, ya ba su, dukkansu kuwa suka shassha.

24. Sa'an nan ya ce musu, “Wannan jinina ne na tabbatar da alkawari, wanda za a bayar saboda mutane da yawa.

25. Hakika, ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranan nan da zan sha wani sabo a Mulkin Allah.”

26. Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.

27. Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe ne, domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumaki kuwa su fasu.’

28. Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.”

29. Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe, ni kam, ba zan yi ba.”

30. Sai Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.”

Karanta cikakken babi Mar 14