Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 14:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sauran kwana biyu a yi Idin Ƙetarewa da idin abinci marar yisti, sai manyan firistoci da malaman Attaura suka nemi hanyar kama Yesu da makirci, su kashe shi,

2. don sun ce, “Ba dai a lokacin idi ba, don kaɗa jama'a su yi hargitsi.”

3. Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana cin abinci ke nan, sai ga wata mace ta zo da wani ɗan tulu na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tsadar gaske. Sai ta fasa ulun, ta tsiyaye masa man a kā.

4. Waɗansu kuwa da suka ji haushi, suka ce wa juna, “Mene ne na ɓata mai haka?

5. Gama da ma an sayar da shi fiye da dinari ɗari uku, an ba gajiyayyu!” Sai suka hasala da ita, suna gunaguni.

6. Amma Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Don me kuke damunta? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.

7. Kullum kuna tare da gajiyayyu, ko yaushe kuma kuke so, kwa iya yi musu alheri, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.

8. Ta yi iyakacin ƙoƙarinta. Ta shafe jikina da mai gabannin jana'izata.

9. Hakika kuwa ina gaya muku, duk inda za a yi bishara a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa domin tunawa da ita.”

10. Sai Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin sha biyun nan, ya je wurin manyan firistoci don ya bashe shi a gare su.

11. Da suka ji haka suka yi murna, har suka yi alkawarin su ba shi kuɗi. Shi kuwa ya riƙa neman hanyar bashe shi.

Karanta cikakken babi Mar 14