Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 13:17-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci!

18. Ku yi addu'a kada abin nan ya auku da damuna.

19. A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon halittar da Allah ya yi, har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.

20. Da ba don Ubangiji ya taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan da ya zaɓa, sai ya taƙaita kwanakin.

21. To, a lokacin nan kowa ya ce muku, ‘Kun ga, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Kun ga, ga shi can!’ kada ku yarda.

22. Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma, in zai yiwu.

23. Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.”

24. “Amma lokacin nan, wato bayan tsabar wahalan nan, za a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba.

25. Taurari za su riƙa faɗawa daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.

26. A sa'an nan ne za a ga Ɗan Mutum na zuwa cikin gajimare, da iko mai girma da ɗaukaka.

27. Sa'an nan zai aiko mala'ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato daga iyakar duniya har ya zuwa iyakar sama.”

Karanta cikakken babi Mar 13