Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 12:36-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Domin Dawuda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce,‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,Zauna a damana,Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’

37. Dawuda da kansa ya kira shi Ubangiji. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?” Babban taron mutane kuwa sun saurare shi da murna.

38. A koyarwa tasa har ya ce, “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishe su a kasuwa,

39. da kuma mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki.

40. Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, da yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”

41. Sai ya zauna gaban baitulmalin Haikalin, yana duban yadda jama'a suke zuba kuɗi a ciki. Waɗansu masu arziki da yawa suna zuba kuɗi masu tsoka.

42. Sai ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta zo, ta zuba rabin kobo biyu a ciki, wato kobo ke nan.

43. Sai ya kira almajiransa, ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiya gwauruwan nan ta zuba cikin baitulmalin nan ya fi na sauran duka.

44. Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk abin da take da shi, duk ma da kuɗinta na abinci.”

Karanta cikakken babi Mar 12