Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 12:26-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Game da tashin matattu kuma, ashe, ba ku taɓa karantawa a Littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa, ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu’?

27. Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Kun ɓata da gaske.”

28. Sai wani malamin Attaura ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu ya ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wane umarni ne mafi girma duka?”

29. Yesu ya amsa masa ya ce, “Mafi girma shi ne, ‘Ku saurara, ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

30. Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, da kuma dukkan ƙarfinka.’

31. Mabiyinsa shi ne, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’ Ba fa sauran wani umarni da ya fi waɗannan girma.”

32. Sai malamin Attaura ya ce masa, “Hakika gaskiyarka Malam, Ubangiji ɗaya ne, ba kuwa wani sai shi.

33. A ƙaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukan hankali, da dukkan ƙarfi, a kuma ƙaunaci ɗan'uwa kamar kai, ai, ya fi dukkan hadayar ƙone-ƙone da yanke-yanke nesa.”

34. Da Yesu ya ga ya yi masa magana da fasaha, sai ya ce masa, “Ba ka nesa da Mulkin Allah.” Bayan wannan kuma ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.

35. Sa'ad da Yesu yake koyarwa a Haikalin sai ya ce, “Ƙaƙa malaman Attaura za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?

36. Domin Dawuda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce,‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,Zauna a damana,Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’

37. Dawuda da kansa ya kira shi Ubangiji. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?” Babban taron mutane kuwa sun saurare shi da murna.

Karanta cikakken babi Mar 12