Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 12:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.

2. Da kakar inabin ta yi, sai ya aiki wani bawansa wurin manoman nan ya karɓo masa gallar garkar.

3. Manoman kuwa suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hanu banza.

4. Sai ya sāke aika musu wani bawa. Shi kuma suka yi masa rotsi, suka wulakanta shi.

5. Ya sāke aiken wani, shi kam, sai suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da waɗansu da yawa, ana dūkan waɗansu, ana kashe waɗansu.

6. Har yanzu dai yana da sauran ɗaya tak, shi ne makaɗaicin ɗansa. Daga ƙarshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’

7. Amma manoman nan suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Ku zo mu kashe shi, gādon yă zama namu.’

8. Sai suka kama shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge.

Karanta cikakken babi Mar 12