Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 12:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.

2. Da kakar inabin ta yi, sai ya aiki wani bawansa wurin manoman nan ya karɓo masa gallar garkar.

3. Manoman kuwa suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hanu banza.

4. Sai ya sāke aika musu wani bawa. Shi kuma suka yi masa rotsi, suka wulakanta shi.

5. Ya sāke aiken wani, shi kam, sai suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da waɗansu da yawa, ana dūkan waɗansu, ana kashe waɗansu.

6. Har yanzu dai yana da sauran ɗaya tak, shi ne makaɗaicin ɗansa. Daga ƙarshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’

7. Amma manoman nan suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Ku zo mu kashe shi, gādon yă zama namu.’

8. Sai suka kama shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge.

9. To, me ubangijin garkan nan zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.

10. Ashe, ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba? cewa,‘Dutsen da magina suka ƙi,Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.

11. Wannan aikin Ubangiji ne,A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’ ”

12. Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi misalin, amma suna jin tsoron jama'a. Don haka suka ƙyale shi, suka tafi.

13. Suka aiko masa da waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus, don su burma shi cikin magana tasa.

14. Da suka zo, suka ce masa, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, ba ka kuma zaɓen kowa, domin ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?

Karanta cikakken babi Mar 12