Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 1:9-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun.

10. Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu yana sauko masa kamar kurciya.

11. Aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai.”

12. Nan da nan sai Ruhu ya iza shi jeji.

13. Yana jeji har kwana arba'in, Shaiɗan na gwada shi, yana tare da namomin jeji, mala'iku kuma suna yi masa hidima.

14. To, bayan an tsare Yahaya, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin bisharar Allah,

15. yana cewa, “Lokaci ya yi, Mulkin Allah ya kusato. Ku tuba, ku gaskata da bishara.”

16. Yana wucewa ta bakin Tekun Galili, sai ya ga Bitrus da Andarawas ɗan'uwansa, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.

17. Yesu ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”

18. Nan da nan kuwa suka watsar da tarunansu, suka bi shi.

19. Da ya ci gaba kaɗan, sai ya ga Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirginsu suna gyaran taruna.

20. Nan da nan da ya kira su, suka bar ubansu Zabadi a cikin jirgin tare da ma'aikata, suka bi shi.

21. Suka shiga Kafarnahum. Ran Asabar kuwa, ya shiga majami'a yana koyarwa.

22. Sun yi mamakin koyarwa tasa, domin yana koya musu da hakikan cewa, ba kamar malaman Attaura ba.

23. Nan take sai ga wani mutum mai baƙin aljan a majami'arsu, yana ihu,

24. yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”

25. Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Yi shiru! Rabu da shi!”

26. Sai baƙin aljanin ya buge shi, jikinsa na rawa, ya yi ihu, ya rabu da shi.

Karanta cikakken babi Mar 1