Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 1:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Farkon bisharar Yesu Almasihu, Ɗan Allah, ke nan.

2. Yadda yake a rubuce a littafin Annabi Ishaya cewa,“Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,Wanda zai shirya maka hanya.

3. Muryar mai kira a jeji tana cewa,Ku shirya wa Ubangiji tarfarki,Ku miƙe hanyoyinsa.”

4. Yahaya Maibaftisma ya bayyana a jeji, yana wa'azi mutane su tuba a yi musu baftisma domin a gafarta musu zunubansu.

5. Sai duk mutanen ƙasar Yahudiya, da dukan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa, suna bayyana zunabansu, yana yi musu baftisma a Kogin Urdun.

6. Yahaya kuwa na sanye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.

7. Ya yi wa'azi ya ce, “Wani na zuwa bayana wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in sunkuya in ɓalle ba.

8. Ni da ruwa na yi muku baftisma, amma shi da Ruhu Mai Tsarki zai yi muku.”

9. Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun.

10. Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu yana sauko masa kamar kurciya.

11. Aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai.”

12. Nan da nan sai Ruhu ya iza shi jeji.

13. Yana jeji har kwana arba'in, Shaiɗan na gwada shi, yana tare da namomin jeji, mala'iku kuma suna yi masa hidima.

Karanta cikakken babi Mar 1