Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 9:51-62 Littafi Mai Tsarki (HAU)

51. Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima.

52. Sai ya aiki jakadu su riga shi gaba, suka kuwa tafi suka shiga wani ƙauyen Samariyawa su shisshirya masa.

53. Amma Samariyawa suka ƙi karɓarsa, domin niyyarsa duk a kan Urushalima take.

54. Da almajiransa Yakubu da Yahaya suka ga haka suka ce, “Ya Ubangiji, ko kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama ta lashe su?”

55. Amma ya juya, ya tsawata musu.

56. Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauye.

57. Suna tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka duk inda za ka.”

58. Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”

59. Ya kuma ce wa wani, “Bi ni.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”

60. Sai Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanar da Mulkin Allah.”

61. Wani kuma ya ce, “Ya Ubangiji, zan bi ka, amma ka bar ni tukuna in yi wa mutanen gida bankwana.”

62. Yesu ya ce masa “Wanda ya fara huɗa da keken noma, yana duban baya, bai dace da Mulkin Allah ba.”

Karanta cikakken babi Luk 9