Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 9:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai ya tara goma sha biyun nan ya ba su iko da izini kan dukan aljannu, su kuma warkar da cuce-cuce,

2. ya kuma aike su su yi wa'azin Mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.

3. Ya kuma ce musu, “Kada ku ɗauki wani guzuri a tafiyarku, ko sanda, ko burgami, ko gurasa, ko kuɗi. Kada kuma ku ɗauki taguwa biyu.

4. Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.

5. Duk waɗanda ba su yi na'am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”

6. Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin bishara, suna warkarwa a ko'ina.

Karanta cikakken babi Luk 9