Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 7:22-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Sai ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.

23. Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”

24. Baya jakadun Yahaya sun tafi, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?

25. To, kallon me kuka je yi? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon gaske, masu zaman annashuwa, a fāda suke.

26. To, kallon me kuka je yi? Annabi? Hakika, ina gaya muku, har ya fi annabi nesa.

27. Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa,‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,Wanda zai shirya maka hanya gabaninka.’

28. Ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”

29. Da duk jama'a da masu karɓar haraji suka ji haka, suka tabbata Allah mai adalci ne, aka yi musu baftisma da baftismar Yahaya.

30. Amma Farisiyawa da masanan Attaura suka shure abin da Allah yake nufinsu da shi, da yake sun ƙi ya yi musu baftisma.

31. “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Waɗanne iri ne su?

Karanta cikakken babi Luk 7