Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 6:20-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sai ya ɗaga kai, ya dubi almajiransa, ya ce,“Albarka tā tabbata gare ku, ku matalauta, domin Mulkin Allah naku ne.

21. “Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da kuke.“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.

22. “Albarka tā tabbata a gare ku sa'ad da mutane suka ƙi ku, suka kuma ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum.

23. Ku yi farin ciki a wannan rana, ku yi tsalle don murna, domin ga shi, sakamakonku mai yawa ne a Sama. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawa.

24. “Amma kaitonku, ku masu arziki domin kun riga kun sami taku ta'aziyya.

25. “Kaitonku, ku da kuke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa. “Kaitonku, ku masu dariya a yanzu, don za ku yi baƙin ciki, ku yi kuka.

26. “Kaitonku in kowa na yabonku. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan ƙarya.”

27. “Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri.

28. Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu'a.

29. Wanda ya mare ka a kunci ɗaya, juya masa ɗaya kuncin kuma. Wanda ya ƙwace maka mayafi, kada ka hana masa taguwarka ma.

30. Duk wanda ya roƙe ka, ka ba shi. Wanda kuma ya ƙwace maka kaya, kada ka neme shi.

31. Yadda kuke so mutane su yi muku, to, ku yi musu haka.

32. In masoyanku kawai kuke ƙauna wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma suna ƙaunar masoyansu.

33. In kuma sai waɗanda suke muku alheri kawai kuke yi wa alheri, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma haka suke yi.

Karanta cikakken babi Luk 6