Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 6:18-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, aka warkar da su.

19. Duk taron suka nema su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.

20. Sai ya ɗaga kai, ya dubi almajiransa, ya ce,“Albarka tā tabbata gare ku, ku matalauta, domin Mulkin Allah naku ne.

21. “Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da kuke.“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.

22. “Albarka tā tabbata a gare ku sa'ad da mutane suka ƙi ku, suka kuma ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum.

23. Ku yi farin ciki a wannan rana, ku yi tsalle don murna, domin ga shi, sakamakonku mai yawa ne a Sama. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawa.

Karanta cikakken babi Luk 6