Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 4:27-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. A zamanin Annabi Elisha kuma akwai kutare da yawa a Isra'ila, ba kuwa ɗayansu da aka tsarkake sai Na'aman, mutumin Suriya, kaɗai.”

28. Da suka ji haka, duk waɗanda suke a majami'a suka husata ƙwarai.

29. Sai suka tashi suka fitar da shi bayan gari, har suka kai shi goshin dutsen da aka gina garinsu a kai, don su jefa shi ƙasa.

30. Amma ya ratsa ta tsakiyarsu, ya yi tafiyarsa.

31. Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a ƙasar Galili, yana koya musu ran Asabar.

32. Suka yi mamakin koyarwarsa domin magana tasa da hakikancewa take.

33. A majami'ar kuwa akwai wani mutum mai baƙin aljan. Sai ya ta da murya da ƙarfi ya ce,

34. “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”

35. Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Shiru! Rabu da shi!” Bayan da aljanin ya fyaɗa shi ƙasa a tsakiyarsu, ya rabu da shi, bai kuwa cuce shi ba.

36. Sai mamaki ya kama su duka, suna ce wa juna, “Wannan wace irin magana ce? Ga shi, da tabbatarwa, da gabagaɗi kuma yake umartar baƙaƙen aljannu, suna kuwa fita.”

37. Labarinsa duk ya bazu ko'ina a kewayen ƙasar.

Karanta cikakken babi Luk 4