Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 3:12-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Masu karɓar haraji ma suka zo a yi musu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?”

13. Ya ce musu, “Kada ku karɓi fiye da abin da aka umarce ku.”

14. Waɗansu soja ma suka tambaye shi, “To, mu fa, me za mu yi?” Sai ya ce musu, “Kada ku yi wa kowa ƙwace ko ƙazafi. Ku dai dangana da albashinku.”

15. Da yake mutane duk sun zaƙu, kowa yana wuswasi a ransa a game da Yahaya, ko watakila shi ne Almasihu,

16. sai Yahaya ya amsa wa dukansu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yi muku baftisma, amma wani yana zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in ɓalle ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.

17. Ƙwaryar shiƙarsa tana hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkama ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun sai ya ƙone shi a wuta marar mutuwa.”

18. Ta haka, da waɗansu gargaɗi masu yawa, Yahaya ya yi wa jama'a bishara.

19. Amma sarki Hirudus, wanda Yahaya ya tsawata wa a kan maganar Hirudiya, matar ɗan'uwansa, da kuma dukan mugayen ayyukan da ya yi,

20. sai ya ƙara da kulle Yahaya a kurkuku.

21. To, da aka yi wa dukan mutane baftisma, Yesu ma aka yi masa baftisma, yana addu'a ke nan, sai sama ta dāre,

22. Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa da wata kama, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai,”

23. Yesu kuwa sa'ad da ya fara koyarwa, yana da shekara wajen talatin. An ɗauke shi a kan, wai shi ɗan Yusufu ne, wanda yake ɗan Heli,

24. Heli ɗan Matat, Matat ɗan Lawi, Lawi ɗan Malki, Malki ɗan Yanna, Yanna ɗan Yusufu,

25. Yusufu ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Amos, Amos ɗan Nahum, Nahum ɗan Azaliya, Azaliya ɗan Najaya,

26. Najaya ɗan Ma'ata, Ma'ata ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Shimeya, Shimeya ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yahuza,

27. Yahuza ɗan Yowana, Yowana ɗan Refaya, Refaya ɗan Zarubabel, Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ɗan Niri,

28. Niri ɗan Malki, Malki ɗan Addi, Addi ɗan Kosama, Kosama ɗan Almadama, Almadama ɗan Er,

29. Er ɗan Yosi, Yosi ɗan Eliyezer, Eliyezar ɗan Yorima, Yorima ɗan Matat, Matat ɗan Lawi,

30. Lawi ɗan Saminu, Saminu ɗan Yahuza, Yahuza ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yonana, Yonana ɗan Eliyakim,

Karanta cikakken babi Luk 3