Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 24:38-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Sai ya ce musu, “Don me kuka firgita, kuke kuma tantama a zuciyarku?

39. Ku dubi hannuwana da ƙafafuna, ai, ni ne da kaina. Ku taɓa ni, ku ji, don fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”

40. Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.

41. Amma tun suna da sauran shakka saboda tsananin farin ciki da mamaki, sai ya ce musu, “Kuna da wani abinci a nan?”

42. Sai suka ba shi wata tsokar gasasshen kifi.

43. Ya kuwa karɓa, ya ci a gabansu.

44. Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake rubuce game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”

45. Sa'an nan ya wayar da hankalinsu su fahimci Littattafai,

46. ya kuma ce musu, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu,

47. a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.

48. Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.

49. Ga shi, ni zan aiko muku da abin da Ubana ya alkawarta. Amma ku dakata a birni tukuna, har a yi muku baiwar iko daga Sama.”

50. Sai ya kai su waje har jikin Betanya. Ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.

Karanta cikakken babi Luk 24