Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 24:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A ranar farko ta mako kuwa, da asussuba, suka je wurin kabarin da kayan ƙanshi da suka shirya.

2. Sai suka tarar an mirgine dutsen daga kabarin.

3. Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji ba.

4. Tun suna cikin damuwa da abin, sai kawai ga waɗansu mutum biyu a tsaye kusa da su, saye da tufafi masu ƙyalƙyali.

5. Don tsoro, matan suka sunkuyar da kansu ƙasa. Mutanen suka ce musu, “Don me kuke neman rayayye a cikin matattu?

6. Ai, ba ya nan, ya tashi. Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana Galili

7. cewa, ‘Lalle ne a ba da Ɗan Mutum ga mutane masu zunubi, a gicciye shi, a rana ta uku kuma ya tashi’.”

Karanta cikakken babi Luk 24