Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 23:49-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

49. Amma duk idon sani, da kuma matan da suka biyo shi, tun daga ƙasar Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban waɗannan abubuwa.

50. To, akwai wani mutum mai suna Yusufu, mutumin Arimatiya, wani garin Yahudawa, shi ɗan majalisa ne, nagari ne, adali kuma.

51. Shi kuwa dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba, yana kuwa sauraron bayyanar Mulkin Allah.

52. Shi ne ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

53. Sai ya sauko da shi, ya sa shi a likkafanin lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, wanda ba a taɓa sa kowa ba.

54. Ran nan kuwa ranar shiri ce, Asabar kuma ta doso.

55. Matan nan kuwa da suka zo tare da shi daga ƙasar Galili, suka bi baya, suka duba kabarin da yadda kuma aka sa jikinsa.

56. Sai suka koma, suka shirya kayan ƙanshi da man shafawa.Ran Asabar kuwa, sai suka huta bisa ga umarni.

Karanta cikakken babi Luk 23