Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 23:22-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ya sāke faɗa musu, a faɗa ta uku, “Ta wane hali? Wane mugun abu ya yi? Ai, ban sami dalilin kisa a gare shi ba. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”

23. Amma suka yi ta matsa lamba, suna ɗaga murya, suna cewa a gicciye shi, har surutunsu ya yi rinjaye.

24. Sai Bilatus ya zartar da hukunci a biya musu bukata.

25. Ya kuwa sakar musu wanda suka roƙa, wato, wanda aka jefa a kurkuku a kan laifin tawaye da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu, su yi masa abin da suke so.

26. Suna tafiya da Yesu yake nan, sai suka cafke wani, mai suna Saminu Bakurane, yana zuwa daga ƙauye, suka ɗora masa gicciye, yă ɗauka ya bi Yesu.

27. Sai taron mutane masu yawan gaske suka bi shi, da waɗansu mata da suke kuka, suke kuma gunji saboda shi.

28. Amma Yesu ya juya gare su, ya ce, “Ya ku matan Urushalima, ku bar yi mini kuka, sai dai ku yi wa kanku da kuma 'ya'yanku,

29. don lokaci na zuwa da za su ce, ‘Albarka tā tabbata ga matan da suke bakararru, waɗanda ba su taɓa haihuwa ba, waɗanda kuma ba a taɓa shan mamansu ba.’

30. Sa'an nan ne za su fara ce wa manyan duwatsu, ‘Ku faɗo a kanmu,’ su kuma ce da tsaunuka, ‘Ku binne mu.’

31. In fa irin abubuwan nan suna faruwa ga ɗanye, yaya zai zama ga ƙeƙasasshe?”

32. Waɗansu mutum biyu kuma masu laifi, aka kai su a kashe su tare da shi.

Karanta cikakken babi Luk 23