Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 23:11-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.

12. A ran nan sai Hirudus da Bilatus suka yi sulhu, don dā abokan gāba ne.

13. Bilatus ya tara manyan firistoci da shugabanni da kuma jama'a,

14. ya ce masu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan, wai yana ɓad da jama'a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi a ƙararrakinsa da kuka kawo ba.

15. Hirudus ma bai samu ba, don ya komo mana da shi. Ga shi kuwa, bai yi wani abu da ya cancanci kisa ba.

16. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”[

17. A lokacin idi kuwa lalle ne ya sakar musu ɗaurarre guda.]

18. Amma duk suka ɗauki ihu gaba ɗaya, suna cewa, “A yi da wannan ɗin, a sakar mana Barabbas!”

19. (Barabbas shi ne wani mutum da aka jefa a kurkuku, saboda wani tawayen da aka yi a birni, da kuma kisankai.)

20. Sai Bilatus ya sāke yi musu magana, don yana so ya saki Yesu.

21. Amma suka yi ta ƙwala ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”

22. Ya sāke faɗa musu, a faɗa ta uku, “Ta wane hali? Wane mugun abu ya yi? Ai, ban sami dalilin kisa a gare shi ba. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”

23. Amma suka yi ta matsa lamba, suna ɗaga murya, suna cewa a gicciye shi, har surutunsu ya yi rinjaye.

24. Sai Bilatus ya zartar da hukunci a biya musu bukata.

25. Ya kuwa sakar musu wanda suka roƙa, wato, wanda aka jefa a kurkuku a kan laifin tawaye da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu, su yi masa abin da suke so.

Karanta cikakken babi Luk 23