Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 22:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Suka ce masa, “Ina kake so mu shirya?”

10. Ya ce musu, “Ga shi, da shigarku gari, za ku gamu da wani mutum ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi har zuwa cikin gidan da ya shiga.

11. Ku ce wa maigidan, ‘Malam ya ce, ina masaukin da zai ci Jibin Ƙetarewa da almajiransa?’

12. Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.”

13. Sai suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.

14. Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, manzanninsa kuma suna tare da shi.

15. Ya ce musu, “Ina so ƙwarai ko dā ma in ci jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya.

16. Gama ina gaya muku ba zan ƙara cin sa ba, sai an cika shi a Mulkin Allah.”

17. Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan, ku shassha.

18. Ina gaya muku, daga yanzu, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya bayyana.”

19. Sai ya ɗauki gurasa, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka, domin tunawa da ni.”

20. Haka kuma, bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a bayar dominku.

Karanta cikakken babi Luk 22