Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

An Ƙulla Shawara gāba da Yesu

1. To, idin abinci marar yisti, wanda ake ce da shi Idin Ƙetarewa, ya gabato.

2. Sai manyan firistoci da malaman Attaura suka yi ta neman yadda za su kashe shi, amma kuwa suna tsoron jama'a.

3. Sai Shaiɗan ya shiga Yahuza, wanda ake kira Iskariyoti, ɗaya daga cikin sha biyun nan.

4. Sai ya tafi ya yi shawara da manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali a kan yadda zai bāshe shi a gare su.

5. Sai suka yi murna, suka kuma yi alkawarin ba shi kuɗi.

6. Shi kuwa ya yarda, ya kuma nemi hanyar bāshe shi a gare su bayan idon jama'a.

Yesu Ya Ci Jibin Ƙetarewa tare da Almajiransa

7. Sai ranar idin abinci marar yisti ta zo, wato, rana da ake yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa.

8. Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce musu, “Ku je ku shirya mana Jibin Ƙetarewa mu ci.”

9. Suka ce masa, “Ina kake so mu shirya?”

10. Ya ce musu, “Ga shi, da shigarku gari, za ku gamu da wani mutum ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi har zuwa cikin gidan da ya shiga.

11. Ku ce wa maigidan, ‘Malam ya ce, ina masaukin da zai ci Jibin Ƙetarewa da almajiransa?’

12. Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.”

13. Sai suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.

Cin Jibin Ubangiji

14. Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, manzanninsa kuma suna tare da shi.

15. Ya ce musu, “Ina so ƙwarai ko dā ma in ci jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya.

16. Gama ina gaya muku ba zan ƙara cin sa ba, sai an cika shi a Mulkin Allah.”

17. Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan, ku shassha.

18. Ina gaya muku, daga yanzu, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya bayyana.”

19. Sai ya ɗauki gurasa, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka, domin tunawa da ni.”

20. Haka kuma, bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a bayar dominku.

21. Amma ga shi, mai bashe ni ɗin nan yana ci a akushi ɗaya da ni.

22. Lalle Ɗan Mutum zai ƙaura kamar yadda aka ƙaddara, duk da haka, kaiton mutumin nan da yake ba da shi!”

23. Sai suka fara tambayar juna ko wane ne a cikinsu zai yi haka.

Mūsū a kan Ko wane ne Babba

24. Sai musu ya tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne babbansu.

25. Sai ya ce musu, “Sarakunan al'ummai sukan nuna musu iko, mahukuntansu kuma sukan nema a ce da su, ‘Mataimakan jama'a.’

26. Amma ku kam ba haka ba. Sai dai wanda yake babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuwa yă zama kamar mai hidima.

27. Wa ya fi girma? Wanda ya zauna cin abinci, ko kuwa mai hidimar? Ashe, ba wanda ya zauna cin abinci ba ne? Ga shi kuwa, ina a cikinku kamar mai hidima.

28. “Ku ne kuka tsaya gare ni a gwaje-gwajen da na sha.

29. Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka, ni ma nake ba ku iko,

30. ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyai, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.

Bitrus zai yi Mūsun Sanin Yesu

31. “Bitrus, ya Bitrus, Shaiɗan ya nemi izinin sheƙe ku kamar alkama, ya kuwa samu.

32. Ni kuwa na yi maka addu'a, kada bangaskiyarka ta kāsa. Kai kuma, bayan da ka juyo, sai ka ƙarfafa 'yan'uwanka.”

33. Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, a shirye nake in bi ka har cikin kurkuku, ko kuma Lahira.”

34. Yesu ya ce, “Ina dai gaya maka Bitrus, a yau ma, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

Jakar Kuɗi, Burgami da Takobi

35. Ya kuma ce musu, “Sa'ad da na aike ku ba kuɗi a ɗamararku, ba burgami, ba takalma, akwai abin da kuka rasa?” Suka ce, “Babu.”

36. Ya ce musu, “Amma a yanzu duk mai jakar kuɗi yă ɗauka, haka kuma mai burgami. Wanda kuwa ba shi da takobi, ya sayar da mayafinsa ya saya.

37. Ina dai gaya muku, lalle ne a cika wannan Nassi a kaina cewa, ‘An lasafta shi a cikin masu laifi.’ Gama abin da aka faɗa a kaina, tabbatarsa ta zo.”

38. Sai suka ce, “Ya Ubangiji, ai, ga takuba biyu.” Ya ce musu, “Ya isa.”

Yesu Ya Yi Addu'a a Gatsemani

39. Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun, kamar yadda ya saba. Almajiransa kuwa suka bi shi.

40. Da ya iso wurin, ya ce musu, “Ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.”

41. Sai ya ɗan rabu da su misalin nisan jifa, ya durƙusa, ya yi addu'a.

42. Ya ce, “Ya Uba, in dai ka yarda, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi” [

43. Sai wani mala'ika ya bayyana a gare shi daga Sama, yana ƙarfafa shi.

44. Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu'a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.]

45. Da ya tashi daga addu'a, ya koma wurin almajiran, ya tarar suna barci saboda baƙin ciki.

46. Sai ya ce musu, “Don me kuke barci? Ku tashi, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.”

An Ba da Yesu, an Kama Shi

47. Kafin ya rufe baki, sai ga taron jama'a suka zo, mutumin da ake kira Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, yake musu jagaba. Sai ya matso kusa da Yesu, don ya sumbace shi.

48. Amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, ashe, da sumba za ka ba da Ɗan Mutum?”

49. Da na kusa da shi suka ga abin da za a yi, suka ce, “Ya Ubangiji, mu yi sara da takuba ne?”

50. Sai ɗayansu ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama.

51. Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkar da shi.

52. Yesu kuma ya ce wa waɗanda suka tasar masa, wato, manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali da shugabannin jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake, kamar masu kama ɗan fashi?

53. Sa'ad da nake tare da ku kowace rana a cikin Haikali, ba ku miƙa hannu garin ku kama ni ba. Amma wannan lokacinku ne da na ikon duhu.”

Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu

54. Sai suka kama shi, suka tafi da shi, suka kai shi cikin gidan babban firist. Bitrus kuwa yana biye daga nesa nesa.

55. Da suka hura wuta a tsakar gida suka zazzauna, Bitrus ma ya zauna a cikinsu.

56. Sai wata baranya ta gan shi zaune a hasken wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Ai, mutumin nan ma, tare da shi yake.”

57. Amma ya musa ya ce, “Ke, ban ma san shi ba.”

58. Bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, sai wani ya gan shi, ya ce, “Kai ma, ai, ɗayansu ne.” Amma Bitrus ya ce, “Ya mutum, ba haka ba ne.”

59. Bayan wajen sa'a guda sai wani ya nace, ya ce, “Ba shakka mutumin nan ma tare da shi yake, don Bagalile ne.”

60. Amma Bitrus ya ce, “Haba, ban ma san abin da kake faɗa ba.” Nan take, kafin ya rufe baki, sai zakara ya yi cara.

61. Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Ubangiji ya faɗa masa cewa, “A yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

62. Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

An Yi wa Yesu Ba'a, an Dūke Shi

63. Sai mutanen da suke riƙe da Yesu suka yi ta masa ba'a, suna dūkansa.

64. Suka ɗaure masa idanu, suka tambaye shi, suka ce, “Yi annabci! Wa ya buge ka?”

65. Suka kuma yi ta masa baƙaƙen maganganu masu yawa, suna zaginsa.

Yesu a gaban 'Yan Majalisa

66. Da gari ya waye sai majalisar shugabannin jama'a ta haɗu, da manyan firistoci da kuma malaman Attaura. Suka kai shi ɗakin majalisarsu suka ce,

67. “To, in kai ne Almasihu, gaya mana.” Amma ya ce musu, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ba.

68. In kuma na yi muku tambaya, ba za ku mai da jawabi ba.

69. Amma nan gaba, Ɗan Mutum zai zauna dama na Allah Mai iko.”

70. Duk suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗa, ni ne.”

71. Sai suka ce, “Wace shaida kuma za mu nema? Ai, mun ji da kanmu daga bakinsa.”