Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 22:42-55 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. Ya ce, “Ya Uba, in dai ka yarda, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi” [

43. Sai wani mala'ika ya bayyana a gare shi daga Sama, yana ƙarfafa shi.

44. Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu'a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.]

45. Da ya tashi daga addu'a, ya koma wurin almajiran, ya tarar suna barci saboda baƙin ciki.

46. Sai ya ce musu, “Don me kuke barci? Ku tashi, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.”

47. Kafin ya rufe baki, sai ga taron jama'a suka zo, mutumin da ake kira Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, yake musu jagaba. Sai ya matso kusa da Yesu, don ya sumbace shi.

48. Amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, ashe, da sumba za ka ba da Ɗan Mutum?”

49. Da na kusa da shi suka ga abin da za a yi, suka ce, “Ya Ubangiji, mu yi sara da takuba ne?”

50. Sai ɗayansu ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama.

51. Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkar da shi.

52. Yesu kuma ya ce wa waɗanda suka tasar masa, wato, manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali da shugabannin jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake, kamar masu kama ɗan fashi?

53. Sa'ad da nake tare da ku kowace rana a cikin Haikali, ba ku miƙa hannu garin ku kama ni ba. Amma wannan lokacinku ne da na ikon duhu.”

54. Sai suka kama shi, suka tafi da shi, suka kai shi cikin gidan babban firist. Bitrus kuwa yana biye daga nesa nesa.

55. Da suka hura wuta a tsakar gida suka zazzauna, Bitrus ma ya zauna a cikinsu.

Karanta cikakken babi Luk 22