Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 20:20-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sai suka yi ta haƙwansa, suka aiki 'yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu adalci ne, da nufin su kama shi a maganarsa, su kuma ba da shi ga mai mulki ya hukunta shi.

21. Suka tambaye shi suka ce, “Malam, ai, mun sani maganarka da koyarwarka duk gaskiya ne. Ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi.

22. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa babu?”

23. Shi kuwa ya gane makircinsu, ya ce musu,

24. “Ku nuna mini dinari. Surar wa da sunan wa yake a jikinsa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.”

25. Sai ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”

26. Sai suka kasa kama shi a kan wannan magana gaban mutane. Saboda kuma mamakin amsarsa, suka yi shiru.

27. Sai waɗansu Sadukiyawa suka zo wurinsa (su da suke cewa, ba tashin matattu),

28. suka tambaye shi suka ce, “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.

29. To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farko ya yi aure, ya mutu bai bar na baya ba.

Karanta cikakken babi Luk 20