Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 2:10-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai mala'ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane.

11. Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji.

12. Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri rufe da zanen goyo, kwance a komin dabbobi.”

13. Ba labari sai ga taron rundunar Sama tare da mala'ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa,

14. “Ɗaukaka ga Allah ta tabbata, can cikin Sama mafi ɗaukaka.A duniya salama ta tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa.”

15. Da mala'iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu.”

16. Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn kwance a komin dabbobi.

17. Da suka gan shi, suka bayyana maganar da aka faɗa musu game da wannan ɗan yaro.

18. Duk waɗanda suka ji kuma, suka yi ta al'ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu.

19. Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci.

20. Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

Karanta cikakken babi Luk 2