Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 19:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yesu ya shiga Yariko. Yana ratsa garin,

2. sai wani mutum mai suna Zakka, babba ne a cikin masu karɓar haraji, mai arziki ne kuma,

3. ya nemi ganin ko wane ne Yesu, amma ya kasa ganinsa saboda taro, don shi gajere ne.

4. Sai ya yi gaba a guje, ya hau wani durumi don ya gan shi, don Yesu ta nan zai bi.

5. Da Yesu ya iso wurin, ya ɗaga kai ya ce masa, “Zakka, yi maza ka sauko, domin yau lalle a gidanka zan sauka.”

6. Sai ya yi hanzari ya sauko, ya karɓe shi da murna.

7. Da suka ga haka, duk suka yi ta gunaguni, suka ce, “A! A gidan mai zunubi dai ya sauka!”

8. Sai Zakka ya miƙe, ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ka ga, rabin mallakata zan ba gajiyayyu. Kowa na zalunta kuwa, zan mayar masa da ninki huɗu.”

9. Yesu ya ce masa, “Yau kam, ceto ya sauka a gidan nan, tun da yake shi ma ɗan Ibrahim ne.

10. Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”

11. Da suka ji abubuwan nan, Yesu ya ci gaba da gaya musu wani misali, gama yana kusa da Urushalima, suna kuma tsammani Mulkin Allah zai bayyana nan da nan.

12. Sai ya ce, “Wani mutum mai asali ya tafi wata ƙasa mai nisa neman sarauta yă dawo.

Karanta cikakken babi Luk 19