Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 18:37-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne yake wucewa.”

38. Sai ya ɗaga murya ya ce, “Ya Yesu Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

39. Sai waɗanda suke gaba suka kwaɓe shi ya yi shiru. Amma ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

40. Sai Yesu ya tsaya, ya yi umarni a kawo shi wurinsa. Da ya zo kusa, ya tambaye shi,

41. “Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ya Ubangiji, in sami gani!”

42. Yesu ya ce masa, “Karɓi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.”

43. Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.

Karanta cikakken babi Luk 18