Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 18:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai.

2. Ya ce, “A wani gari an yi wani alƙali marar tsoron Allah, marar kula da mutane.

3. A garin nan kuwa da wata wadda mijinta ya mutu, sai ta riƙa zuwa wurinsa, tana ce masa, ‘Ka shiga tsakanina da abokin gābana.’

4. Da fari ya ƙi, amma daga baya sai ya ce a ransa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane,

5. amma saboda gwauruwar nan ta dame ni, sai in bi mata hakkinta, don kada ta gajishe ni da yawan zuwa.’ ”

6. Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan marar gaskiya ya faɗa!

7. Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?

8. Ina gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa'ad da Ɗan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya ne?”

9. Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce,

10. “Waɗansu mutum biyu suka shiga Haikali yin addu'a, ɗaya Bafarisiye, ɗaya kuma mai karɓar haraji.

Karanta cikakken babi Luk 18