Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 17:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai ya ce wa almajiransa, “Sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadinsu!

2. Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi a cikin teku.

3. Ku kula da kanku fa. In ɗan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa. In kuwa ya tuba, ka yafe shi.

4. Ko ya yi maka laifi sau bakwai rana ɗaya, sa'an nan ya juyo wurinka sau bakwai ya ce, ‘Na tuba,’ sai ka yafe shi.”

5. Sai manzanni suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya.”

6. Ubangiji kuwa ya ce, “Da kuna da bangaskiya, ko da misalin ƙwayar mastad, da za ku ce wa wannan durumi, ‘Ka ciru, ka dasu cikin teku,’ sai kuwa ya bi umarninku.”

Karanta cikakken babi Luk 17