Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 15:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, sai duk masu karɓar haraji da masu zunubi suka yi ta matsowa wurinsa su saurare shi.

2. Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka riƙa gunaguni suna cewa, “Haba! Wannan mutum yana karɓar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci!”

3. Sai ya ba su wannan misali ya ce.

4. “In waninku yana da tumaki ɗari, ɗayarsu ta ɓace, to, ba sai ya bar tasa'in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta ɓata, har ya same ta ba?

5. In kuwa ya same ta, sai ya saɓo ta a kafaɗa, yana farin ciki.

6. In ya dawo gida, sai ya tara abokansa da maƙwabta ya ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na samo tunkiyata da ta ɓata.’

7. Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”

8. “Ko kuwa wace mace ce, in tana da kuɗi azurfa guda goma, in ta yar da ɗaya, ba sai ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta nacin nemansa, har ta same shi ba?

9. In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da maƙwabta mata, ta ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na sami kuɗin nan da na yar.’

10. Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”

11. Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai 'ya'ya biyu maza.

12. Sai ƙaramin ya ce wa ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gādo.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa.

13. Bayan 'yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha'a.

14. Da ya ɓad da kome kakat, aka yi babbar yunwa a ƙasar, sai ya shiga fatara.

15. Ya je ya rāɓu da wani ɗan ƙasar, shi kuwa ya tura shi makiyayar kiwon alade.

Karanta cikakken babi Luk 15