Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 12:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, za a yi musun saninsa a gaban mala'ikun Allah.

10. Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.

11. Sa'ad da suka kai ku gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,

12. domin Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya kamata ku faɗa a lokacin.”

13. Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, kă ce wa ɗan'uwana ya raba gādo da ni.”

14. Amma Yesu ya ce masa, “Haba kai kuwa, wa ya sa ni in zama muku alƙali, ko in raba muku gādo?”

15. Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.”

16. Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta yi albarka ƙwarai.

17. Sai ya ce a ransa, ‘To, ƙaƙa zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’

18. Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina waɗansu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki.

19. Zan kuma ce wa raina, “Lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagali.” ’

20. Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’

Karanta cikakken babi Luk 12