Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 11:9-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ina dai gaya muku, ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.

10. Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.

11. Wane uba ne a cikinku, da ɗansa zai roƙe shi [gurasa, ya ba shi dutse? Ko ya roƙe shi] kifi, ya ba shi maciji?

12. Ko kuwa ya roƙe shi ƙwai, ya ba shi kunama?

13. To, ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”

14. Wata rana Yesu yana fitar da beben aljan. Da aljanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.

15. Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”

16. Waɗansu kuwa, don su gwada shi, suka nema ya nuna musu wata alama daga Sama.

17. Shi kuwa da ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Haka kuma, in gida ya rabu a kan gāba, zai baje.

18. In kuma Shaiɗan ya rabu a kan gāba, yaya mulkinsa zai ɗore? Ga shi, kun ce da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu.

19. In kuwa da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu, to, 'ya'yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.

20. Ni kuwa in da ikon Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan.

21. In ƙaƙƙarfan mutum ya yi ɗamara sosai, yana tsaron gidansa, kayan gidansa lafiya suke.

Karanta cikakken babi Luk 11